Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar ana fargabar wasu ‘yan ta’addan ISWAP sun kai farmaki sansanonin soji guda biyu a jihar sun tafka mummunar barna.
A ecwar wani rahoton da AFP ta fitar jaridar Leadership kuwa ta tattaro, ‘yan ta’addan sun kai hare-haren ne a ranakun Juma’a da Asabar a wani sansanin soji da kuma gari, inda suka kashe sojoji tara.
Hakazalika, an ce sun hallaka wasu ‘yan sanda biyu da kuma wani adadi na mutanen gari, kamar yadda wata majiya ta shaida.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, mambobin kungiyar ta ISWAP sun zo ne a kan motoci dauke da makamai, inda suka farmaki yankin Malam Fatori a gundumar Abadam a ranakun Juma’a da Asabar.
A cewar wani rahoton SaharaReporters kuma, akalla sojoji 30 ne suka mutu a yayin wannan mummunan hari baya ga lalata kayayyakin aiki da dama na jami’an tsaron.
Kungiyar ta ISWAP ta ce, mayakanta sun mamaye wani yankin garin dauke da makamai, inda suka hallaka mutane 30 da wasu sojoji 30. Hukumar tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin, duk da cewa an samu bambancin rahoto daga ‘yan ta’addan da kuma hukumomin tsaro.
You must log in to post a comment.