Borno: ISWAP Sun Kai Hari Jami’ar Soji

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Dakarun Islamic State in West Africa Province (ISWAP) sun fitar da bidiyon mayakansu su na kai hari a jami’ar sojoji da ke kauyen Buratai, Biu, jihar Borno.

Mayakan na ISWAP sun shiga sashen koyon ilmin yaki na Tukur Yusufu Buratai Institute for War and Peace (TBI) da ke cikin jami’ar sojoji da ke garin Biu inda suka kaddamar da hari.

Rahotanni daga Daily Trust sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kai harin ne a karshen makon nan. A bidiyon za a ga ‘yan ta’addan su na ta harbe-harbe ba tare da samun martani daga sojoji ba. Za a iya ganin motocin sojoji a ajiye babu kowa.

A bidiyon da aka fitar, ‘yan ta’addan sun rika kona tutocin sojojin kasa da na Najeriya, su na yin kabarbari.

Da suka zo inda aka ajiye motocin jami’an sojoji, ‘yan ta’addan sun sauko da tutoci kasa, sun kona su. Za a iya ganin ‘yan ta’addan su na bankawa tutocin wuta. Wannan shi ne hari na biyu da ‘Yan ta’addan suka kai garin Buratai a makon nan.

Labarai Makamanta