Borno: ISWAP Sun Harbe Babban Janar Na Soja

Rahotanni daga Birnin Maiduguri na Jihar Borno, na bayyana cewar an harbe wani babban jami’in soja mai matsayin Birgediya Janar Dzarma Zirkushi har lahira yayin da mayaƙan rundunar dakarun ƙasashen yankin tafkin Chadi, ISWAP, ta yi wa sojoji kwantan ɓauna a jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan Birgediya Janar ɗin, akwai ƙarin sojoji guda huɗu da su ma suka rasa rayukansu a kwantan ɓaunar da ya auku a Bulguma, kilomitoci kaɗan daga garin Askira na ƙaramar hukumar Askira Uba.

Rahotannin sun ƙara da cewa tuni aka tura dakarun 28 Task Force Brigade da ke Chibok domin ƙarfafa tsaro a Askira, wanda ake kai farmaki.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoton yadda mayaƙan ISWAP suka dirar wa garin cikin jerin gwanon manyan motoci masu ɗauke da bindigogi.

Wani ɗan sintiri ya bayyana cewa mayaƙan sun durfafi wani sansanin soji inda suka fara musayar wuta da sojojin.

An yi wa sojojin kwantan ɓauna a sa’ilin da suke kan hanyar kai wa sojojin da ke ɗauki-ba-daɗi da ‘yan tada ƙayar bayan ɗauki.

“Yau ranar baƙin ciki ce a gurinmu a filin daga; mun rasa Birgediya Janar. Mayaƙan ISWAP sun yi wa Birgediya Janar ɗin da sauran sojojin da ke kan hanyarsu ta kai wa sojojinmu da ke Askira ƙarin ƙarfi kwantan ɓauna inda kuma suka harbe su har lahira. Muna cikin ɓacin rai,” wata majiya ta tsaro ta faɗa.

Majiyar ta ƙara da faɗin cewa jiragen yaƙi sun yi ruwan bamabamai a kan ‘yan ƙungiyoyin tada ƙayar bayan.

Labarai Makamanta