Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta musanta rahotannin tashin bam a filin jirgin saman Maiduguri.
Wata sanarwa fa kakakin Hukumar FAAN, Henrietta Yakubu ya fitar, ta ce: “Ba a kai wa filin jirgin saman hari ba, kuma ba a kai hari ko wanne bangarensa ba.”
“Game da rahoton da aka samu ta yanar gizo da ke cewa bam ya tashi a filin jirgi na Maiduguri da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka shirya, hukumar ta FAAN ta sanar da fasinjoji da sauran jama’a cewa babu wani fashewa, ko kutse a filin jirgin Maiduguri.”
Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa an samu fashewar wani abu da sanyin safiyar ranar Asabar a wani gida da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno. Rahoton na Channels ya ce gidan yana kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
Rahoton ya kara da cewa fashewar ta afku a kasa da mita 100 da wani sansanin tubabbun ‘yan Boko Haram, inda gidaje kusan 12 suka lalace.
A Maiduguri dai an samu raguwar hare-haren ‘yan tada kayar baya a ‘yan kwanakin nan.
You must log in to post a comment.