Borno: Gwamna Zulum Ya Kai Ziyarar Bazata Asibiti

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babangana Umara Zulum a ranar Alhamis ya yi basaja ya kai ziyara wasu asibitocin jihar inda ya ga jami’ai na karban kudi N8,000 zuwa N10,000 duk da cewa kyauta ake jinya.

Mai magana da yawun gwamnan ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis a shafinsa na sada zumunta na Facebook.

Yace Zulum ya sammaci Kwamishanar Lafiyan jihar, Mrs. Juliana Bitrus, domin ta raka shi wani waje ba tare da fada mata inda zasu nufa ba. Kai tsaye Zulum ya shiga sabon asibitin da aka gina a Gwange II dake Maiduguri kuma ya tarar ma’aikata na karban N8,000 zuwa N10,000 hannun marasa lafiya masu cuta irin Malariya kafin dubasu.

Zulum yace: “Ma’aikatan da muka samu a nan sun tabbatar mana da cewa ana karbi N8,000 zuwa N10,000 hannun marasa lafiya don basu maganin zazzabin cizon sauro. Kai har sun mayar da asibitin na kudi, shiyasa mutane basu zuwa saboda basu da kudi.” “Kawai suna amsan kudi hannun mutane suna zubawa a aljihu.”

Gwamnan ya umarci hukumar kananan asibitoci ta gudanar da bincike kan lamarin kuma a hukunta ma’aikatan da aka kama da laifi.

Zulum ya yi takaici yayinda ya tarar da ma’aikaci daya kacal a wajen duk da cewa an dauki ma’aikata 29 aiki a asibitin kuma ana biyansu albashi.

Labarai Makamanta