Borno: Gwamna Zulum Ya Biya Wa Dalibai 24,323 Kudin Jarrabawar WAEC

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da sakin naira million dari da hamsin da biyu da digo shida N152.6M na biyan kudin jarabawar dalibai 24,323 na daliban jahar Borno da suka rubuta jarabawar WAEC na bana May/June 2019.

Mai magana da yawun Gwamnan Malam Isa Gusau shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, a cewar sa, kamar yadda Gwamnatin jihar Borno ta saba na biyan kaso 45%, karamar hukuma kuma kaso 30%, da kuma iyayen yara su biya kaso 25% cikin dari na kudin jarabawar.

Gusau yace amincewa da biyan kudin ya biyo biyan izini da sakataren dindin na Ma’aikatar ilimi na jahar Mohammed Mustapha Abacha ya nema.

Gwamnan ya yi fatan daliban jihar za su samu kyakkyawan sakamako a jarabawar da suka rubuta a bana.

Zulum ya yi kira ga Iyayen yara da malaman makaranta su jajirce wurin baiwa dalibai inagantaccen ilimi a jihar.

Related posts