Rahoton dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta ce dakarun tawagar Operation Hadin Kai sun yi nasarar kawar da ‘yan ta’adda sama da 36 a ayyuka daban-daban ta sama a yankin Arewa maso Gabas cikin makwanni biyu.
Daraktan yada labarai na ayyukan soji, Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan a jawabin nasarorin da jami’an tsaro ke samu a ranar Alhamis 22 ga watan Satumba a Abuja.
Sojojin sun farma ‘yan ta’addan Boko Haram, sun hallaka da yawa a jihar Borno Ya ce an kashe Abu Asiya a yankin Parisu, shi kuwa Abu Ubaida an hallaka shi ne a Sheruri duk dai a dajin Sambisa a kwanakin 12 da 15 ga watan Satumba.
A bangare guda, rundunar ta ce ta ceto mutum 130 a hannun ‘yan ta’addan tare da kama ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP 46 da kuma abokan harkallarsu 12.
An kwato bindigogin AK47 guda 21 da alburusai 163 masu girman 7.6mm, bindigogin RPG guda biyu, wasu nau’in bindigogi 25 kayan fashewa guda hudu, kayan haÉ—a bama-bamai 10, keke 23, babura 10 da keke napep daya.
Hakazalika, an kwato wayoyin hannu 19, fitilu 28 buhunnan hatsi, dabbobi 122 da tsabar kudi N203,125. A jumillance, hukumar tsaro ta ce akwai mutum 368 cikin ‘yan ta’addan da suka mika wuya, ciki har da yara, mata da manyan maza.
You must log in to post a comment.