Borno: Dakarun Soji Sun Hallaka Mayakan ISWAP Masu Yawa

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kashe aƙalla mayaƙan ISWAP 24.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewa mayaƙan sun gamu da ajalinsu ne a yayin da suka yi ƙoƙarin kai hari a wani sansanin soji da ke Rann, wanda gari ne da ƴan ƙungiyar Boko Haram suka lalata a baya a jihar Borno.

Sai dai sojin ƙasar sun rasa sojoji biyar yayin wannan bata-kashin da aka yi tsakanin ƴan ISWAP ɗin da kuma sojojin rundunar Operation Hadin Kai.

Har yanzu ana samun hare-haren ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a arewa maso gabashin ƙasar.

Ko a cikin watan Nuwambar da ya gabata sai da ƴan ISWAP din suka kashe wani janar ɗin sojin Najeriyar a jihar Borno da kuma wasu ƙananan sojoji yayin wata bata-kashi da yan tayar da ƙayar bayan.

Labarai Makamanta