Borno: Boko Haram Ta Ƙwace Ƙaramar Hukumar Marte

Mayakan Boko Haram sun kwace iko da garin Marte na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya. Da yammacin ranar Laraba ne Boko Haram din ta kai hari a barikin sojoji da ke Marte inda bayan wani lokaci ana fafatawa, ‘yan Boko Haram din suka ci dunun sojoji suka kuma kwace muggan makamai da motocin yaki daga wurin sojojin Najeriya.

Kimanin sojoji bakwai ne suka rasa rayukansu ciki har da mai mukamin manjo a sanadiyyar arangamar da aka yi. Kazalika ‘yan Boko Haram sun cinna wa barikin sojin na Marte wuta bayan da suka kammala barin wuta da sojoji, a yanzu ma har sun kafe tutocinsu don nuna cewa sun karbe iko da Marte kamar yadda wani soja da bai son a fadi sunansa ya shaida wa gidan rediyon Deutsche Welle na Jamus.

Ba da jimawa ba ne ba dai gwamnatin jihar Borno ta mayar da ‘yan gudun hijira garin na Marte bayan sun kwashe shekaru suna gudun hijira saboda hare-haren da Boko Haram din ta rinka kai musu a shekarun baya. Sai dai kuma a yanzu haka ma labarin da muka samu mutanen garin sun gudu a yayin da Boko Haram ke ci gaba da iko da garin.

Labarai Makamanta