Borno: An Yi Kare Jini Biri Jini Tsakanin Boko Haram Da ISWAP

Wata kafa da ke nuna goyon baya ga kungiyar al-Qaeda ta ba da rahoton cewa ƙungiyoyin ta’adda da ke hamayya da juna sun gwabza faɗa a Najeriya kuma wani ƙazamin faɗa ya ɓarke tsakanin shugabbanin IS a Somalia.

Kafar Thabat ta wallafa labari a mujallarta ta mako mako a kafar RocketChat da ta saba turo labarai game da rikicin.

Ta ce mayakan IS sun gwabza faɗan ne a ƙauyen Sunawa da ke kan iyakar Najeriya da Nijar.

Kuma rikicin ya ɓarke ne bayan mayaƙan IS sun sace mata da dama da ke da alaƙa da Boko Haram inda kuma Boko Haram ta ƙaddamar da hari kan sansanin IS kuma a cewar kafar ta kashe mayaƙan IS da dama tare da kuɓutar da matan.

A 2015 shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya sanar da goyon bayansa ga IS kafin daga baya ɓangaren ƙungiyar ya sauya suna zuwa ISWAP.

Daga baya Shekau da wasu mabiyansa suka ɓalle daga IS bayan ta naɗa sabon shugaba. Kuma an sha bayar da rahotannin faɗa tsakanin ƙungiyoyin a yankin Tafkin Chadi.

Kafar Thabar kuma ta bayar da rahoton cewa an gwabza ƙazamin fada tsakanin mayaƙan IS a Somalia kan neman shugabanci. Kuma a cewar kafar rikicin ya ɓarke ne bayan ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar Abdel Qadir al-Mumin ya kwanta rashin lafiya a watan Disamba.

Labarai Makamanta