Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamna Babagana Zulum na jihar ya bayyana cewa an gano sunayen jarirai yayin aikin tantance ma’aikata da ake yi a karamar hukumar Shani ta jihar Borno.
An ruwaito cewa an gano manyan ma’aikata ne ke karkatar da albashin da ake biyan ma’aikatan na bogi ciki har da jarirai zuwa asusun ajiyar kuɗaɗen su saboda zalunci da son rai.
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a wurin bikin gargajiya ta Menwara a karamar hukumar Shani a ranar Asabar. Gwamna ya ce an gano sunayen jarirai da ke karbar albashi a Borno.
“Bari in fada muku a karkashen aikin tantancewar, an gano sunayen jarirai yayin da ake biyan Naira miliyan 19 ga ma’aikatan bogi a karamar hukumar Shani a duk wata. An gano cewa wani gida daya na da ma’aikatan bogi 300 kuma idan hakan ya cigaba, ina tsoron, karamar hukumar Shani ba za ta iya biyan albashin ma’aikatan ta ba a gaba.”
Gwamnan ya yi taro da Sarkin Shani, Alhaji Muhammadu Nasiru Mailafiya da wasu masu ruwa da tsaki game da lamarin kuma ya umurci kwamishinan kananan hukumomi da Masarautu, Sagum Mai Mele ya tantance aikin ya kuma mayar da ma’aikatan da aka kore su bisa kuskure.
You must log in to post a comment.