Boko Haram Ta Ƙi Sakin Sharibu Ne Domin Haɗa Fitina – Lai

An bayyana cewa da gangan ‘yan ta’addan Boko Haram suka ki sakin matashiyar yarinya mai bin addinin Kirista Leah Sharibu domin raba kan ‘yan Najeriya ta bangaren addini.

Leah Sharibu, wadda iyayenta Kiristoci ne ta kasance ɗaya daga cikin dalibai mata 110 na makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati, Dapchi a jihar Yobe da kungiyar Boko Haram ta sace a shekarar 2018.

Musamman lamarinta ya ja hankalin al’umman kasar da na duniya baki daya, saboda yadda aka saki wasu amma ita aka tsare ta saboda ta ki yin watsi da addininta na Kirista.

Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya Lai Mohammed ya bayyana hakan a tattaunawar da gidan talabijin na Channels TV ya yi dashi. “Yan ta’addan sun san cewa rike Sharibu a hannunsu na iya haifar da rikicin addini a kasar, shi ya sa suka ƙi sakin ta bayan sun saki sauran ‘yan makarantar”.

Ministan ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya na iya bakin kokarin ta wajen ganin an sako ‘yar makarantar Dapchin. Ya bukaci ‘yan Najeriya da kar su yi yarda su fada tarkon ‘yan ta’adda ta hanyar kallon al’amuran tsaro ta fuskar addini ko kabilanci.

Mohammed ya ce: “Don Allah ya zama dole mu kiyaye kuma mu kula sosai a kan yadda muke kallon al’amura. Wannan shi ne ainihin abin da ‘yan ta’addar ke so su yi, su hada Musulmi da Kirista.”

Sharibu, wacce ta kasance kirista mai shekaru 14 a lokacin da aka kama ta, ita kadai ce yar makarantar Dapchi da ta rage a hannun yan ta’addan bayan mamayar da Boko Haram ta kai masu a garin Dapchi da ke jihar Yobe a 2018.

Labarai Makamanta