Boko Haram Sun Kafa Jamhuriya A Jihar Neja

Labarin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta bayyana cewa Boko Haram sun kafa sansanoni a cikin Ƙananan Hukumomin Shiroro da kuma Borgu da ke cikin Jihar.

Sai dai a wannan karon, Gwamnatin Jihar Neja ta ƙara fito da mummunan halin da ake ciki a yankunan, inda a cikin sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Matane ya yi wa manema labarai ranar Talata a Minna, ya ce tuni har ‘yan ta’adda sun fara bi cikin Masallatan Juma’a su na wa’azi a ƙauyuka cewa jama’a su daina tura ‘ya’yan su makarantun boko, kuma a kowa ya tashi ya bijire wa gwamnati.

Matane ya ce a halin da ake ciki, ‘yan bindiga da ‘yan samame sun haɗe kai su na ƙoƙarin yaƙar gwamnati a Shiroro, su na bi masallatan yankunan su na kafirta gwamnati da kuma hana ‘ya’ya mata karatun boko.

“Garuruwan da ISWAP/Boko Haram su ka bi su na wa’azin sun haɗa da Shuluba, Koki, Kusare da Madaka.”

Sakataren Gwamnatin Tarayya ya ce ‘yan ISWAP ɗin har a cikin wa’azin su sukan ce, “Duk waɗanda su ka bi mu za mu kare lafiya da rayukan kowa. Amma abin da mu ke so shi ne ku bi mu a bijire wa gwamnati.”

Matane ya ce kuma su kan ce, “Gwamnati ta sani mu ba masu garkuwa da mutane ba ne. Allah ne ya aiko mu domin mu kafa ‘Daular Musulunci’.”

A cikin bayanin sa, Matane ya ƙara da cewa ISWAP na nan na ta ƙoƙarin kafa sansani a Gandun Dajin Babana da ke cikin Ƙaramar Hukumar Borgu.

Labarai Makamanta