Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Bincike ya bayyana cewa hare-haren da ake yawan kai wa babban titin Abuja zuwa Kaduna duk ‘yan Boko Haram ne suke kai farmakin.
A ranar Lahadi, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da ba a san yawansu ba sannan sun halaka wani fitaccen dan siyasan jihar Zamfara, Sagir Hamidu a wani wuri mai suna Kurmin Kare a kan hanyar.
‘Yan ta’addan sun kara komawa kusa da wurin sannan suka kara budewa wasu matafiya wuta har suka yi garkuwa da wasu.
Masu bayar da bayanan sirri a Abuja sun bayyana wa Daily Nigerian cewa, duk ‘yan Boko Haram ne suka kafa sansani a dajikan Kaduna da na Neja, kuma suke cigaba da kisan mutane.
“Bisa bayanan sirri, an gano cewa ‘yan Boko Haram ne suke da alhakin kai farmaki a wuraren Kurmin Kare dake kan babban titin Abuja zuwa Kaduna. “Su ne suke satar mutane a wuraren Mashegy da Shiroro a jihar Neja.
Suna kokarin ganin sun taru a yankin ne don garkuwa da mutane tare da tara kudade masu tarin yawa. “Sun kafa sansanoninsu a Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi da sauran wurare.
You must log in to post a comment.