Boko Haram Na Kafa Sansanoni A Zamfara – Matawalle

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle ta ce ta samu rahotonnin da ke cewa kungiyar Boko Harama tsagin ISWAP na kokarin kafa sansanoni a kauyen Mutu na gundumar Mada da ke karamar hukumar Gusau a jihar.

Shugaban kwamitin shigar da kara ga laifukan da suka shafi fashin daji kuma mamba a kwamitin tsaro da tattara bayanan sirri na jihar Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Gusau babban birnin jihar.

Ya ce Mambobin ISWAP sun shiga jihar ne ta yankunan Danjibga da Kunchin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe a jihar.

Labarai Makamanta