Boko Haram Na Dab Da Mamaye Birnin Abuja – Gwamnan Neja

Mai girma Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya bayyana cewar yaƙi na neman cinye Jihar Neja daga Mayakan Boko Haram, kuma muddin ba’a gaggauta ɗaukar matakan da suka dace ba ‘yan ta’addan za su mamaye babban birnin tarayya Abuja.

Da yake magana lokacin da ya ziyarci sansanin ‘Yan Gudun Hijira a ranar Litinin, gwamnan ya ce ‘yan ta’addan sun karbe wani yanki na jihar bayan Gwamnatin Tarayya ta gaza a kokarin samar da tsaro a jihar.

Ya ce ya tuntubi Gwamnatin Tarayya a lokuta daban-daban amma babu wani abu mai amfani da ya fito daga kokarinsa

Bello ya yi gargadin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram na kokarin mai da Kaure a karamar hukumar Shirroro da ke jihar ta zama hedikwatarsu kamar yadda suka yi a dajin Sambisa a jihar Borno.

Saboda da haka, ya ce yayin dajin Sambisa ke da nisan kilomita da yawa daga Abuja, tsakanin Kaure da Abuja awanni biyu kawai. “Na nemi taimakon gwamnatin tarayya amma abin takaici lamarin ya kai ga wannan matakin kuma idan ba a kula ba, hatta Abuja ba za ta tsira ba.

Mun dade muna fadin haka amma duk kokarin da ake yi ya zama a banza.” Da yake jawabi kan yawan ‘yan gudun hijirar da ke sansanin, Bello ya ce wasu daga cikinsu sun fara komawa gida yana mai cewa mafi yawansu za su ci gaba da zama a sansanin saboda ‘yan ta’adda sun kwace garuruwansu da kauyukansu

A lokacin ziyarar gwamnan, akwai yara 1,447, mata masu ciki 119 da wasu mata 447 a sansanin, waɗanda bala’in Boko Haram ya raba da muhallinsu.

Labarai Makamanta