Boko Haram: Muna Da Zaratan Sojoji Ba Sai Mun Yi Haya Ba – Buhari

Gwamnatin tarayya ta yi watsi da tattaunawar shigo da sojojin haya na kasashen waje don yaki da masu tayar da kayar baya da sauran nau’ikan rashin tsaro a sassa daban-daban na kasar nan.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (Rtd), ne ya fadi haka a ranar Alhamis yayin wani taron a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce gwamnatin ta gwammace ta yi amfani da dukkanin rundunoni don kawar da matsalar.

Monguno ya bayyanawa manema labarai cewa, Najeriya na da ma’aikata da kayan aiki don cimma nasara kan wadannan kalubalen tsaro na cikin gida, ba tare da sai an yi haya daga waje ba.

“Ra’ayi da umarnin Shugaban kasa shi ne cewa ba za mu shigo da sojojin haya ba alhali muna da mutanenmu da za mu magance wadannan matsalolin. Muna da ma’aikata da kayan aiki, kuma Shugaban kasa ya bai wa sojojin wata sabuwar kwarin gwiwa,” inji shi.

Ya kuma ce, gwamnati ba za ta mika wuya ga yin zagon kasa da amfani da masu aikata laifi ba ta hanyar muzgunawa ‘yan kasa ba tare da wani laifi ba, ya kara da cewa abinda ya fi dacewa shine ta girka duk karfin da ya dace don kawar da masu laifin.

Ya kara da cewa, sauye-sauyen da Shugaba Buhari ya yi a tsarin shugabancin tsaro “ya ba mu kwarin gwiwa cewa abubuwa za su daidaita, ta yadda duk abin da za mu yi game da tsaron Najeriya za su yi daidai da bukatun mu.

Labarai Makamanta