Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ɗan takarar shugabancin ƙasa a babbar jam’iyya adawa ta PDP Atiku Abubakar, yace duk ƙarya ce ake yi kawai, amma babu wani surƙuƙin dajin da ‘yan ta’adda za su iya ɓoyewa a Dajin Sambisa, a ce wai an kasa gano inda su ke.
Atiku ya ce ya shiga dajin, amma babu komai daga ciyayi, sai kalage da gezoji kawai.
Ya ce kan sa na ɗaurewa ganin yadda ake ta gaganiya da Boko Haram, amma an kasa ganin bayan su a Nijeriya.
Atiku ya ce gaba ɗaya ma ya na mamakin salsala, musabbabi da tushen Boko Haram a ƙasar nan.
Ya ce ya rasa yadda aka yi har yanzu su ke kai hare-hare duk kuwa da yadda sojoji ke ta ƙoƙarin kakkaɓe su.
Atiku ya yi wannan mamakin a lokacin da ake taron ganawa da shi, wanda gidan talabijin na Channels TV ya shirya, kuma ya gabatar a ranar Lahadi.
Atiku ya gabatar da shirin ne tare da mataimakin takarar sa, Gwamna Ifeanyi Okowa, na Jihar Delta.
Da ya ke amsa tambaya kan yadda zai magance matsalar tsaro, Atiku ya ce babu wani daji a jihar Barno da za a ce wai ya na da faɗin da zai iya ɓoye Boko Haram tsawon shekaru su ka ta’addanci a yankin. A nan ne ya tuna zaman da ya yi lokacin ya na fatiro a dazukan Arewa maso Gabas, lokacin ya na jami’in Hukumar Kwastan.
“Ni ina da masaniya dangane da kan iyakoki da dazuka. Ni dai ban ga wani daji da har ‘yan ta’adda za su iya ɓoyewa a Jihar Barno ba a gan su ba.
“A gaskiya lamarin Boko Haram ɗin nan fa ya na ɗaure min kai.” Inji Atiku.
“Sun ce wai akwai wani daji Sambisa, to na je dajin Sambisa, amma ban ga wani surƙuƙin daji ba. Kawai ciyawa da kalage da gezoji ne a wurin.”
Yayin da ya ke jinjina wa Sojojin Najeriya, Atiku ya ce ba wani abu zai iya kawar da Boko Haram ba sai shugabanci nagari, wanda zai daƙile wasu ‘ƙadangarun’ cikin sojoji da ‘gizakar’ da ke wajen sojoji.
You must log in to post a comment.