Boko Haram: Jama’a Na Tserewa Daga Jihar Yobe


Jama’a na ci gaba da tserewa daga garin Kanamma na yankin karamar hukumar Yunusari ta jihar Yobe, bayan wani gagarumin hari da ake zargin ƴan kungiyar Boko Haram sun kai garin.

Bayanai sun ce maharan sun ƙona gidaje, suka ɓalle shaguna suka kwashi kayan abinci da na masarufi.

Wani mazauni garin na Kanamma Umara Famfasa, wanda ya sami kwashe iyalinsa suka tsere ya ce mata da yara ƙanana ne ke tserewa suna tsallakawa zuwa Nijar.

Labarai Makamanta