Boko Haram Da ISWAP Sun Kafa Gwamnati A Neja

Labarin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta bayyana cewa Boko Haram sun kafa sansanoni a cikin Ƙananan Hukumomin Shiroro da kuma Borgu da ke cikin Jihar.

A cikin sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Matane ya yi wa manema labarai a Minna, ya ce tuni har ‘yan ta’adda sun fara bi cikin Masallatan Juma’a su na wa’azi a ƙauyuka cewa jama’a su daina tura ‘ya’yan su makarantun boko, kuma a bijire wa gwamnati.

Matane ya ce a halin da ake ciki yanzu Boko Haram da ‘yan bindiga sun haɗe kai su na ƙoƙarin yaƙar gwamnati a Shiroro, su na bi masallatan yankunan su na kafirta gwamnati da kuma hana ‘ya’ya mata karatun boko.

“Garuruwan da ISWAP/Boko Haram su ka bi su na wa’azin sun haɗa da Shuluba, Koki, Kusare da Madaka.”

Matane ya ce kuma su kan ce, “Gwamnati ta sani mu ba masu garkuwa da mutane ba ne. Allah ne ya aiko mu domin mu kafa ‘Daular Musulunci’.”

Labarai Makamanta