Biyan Haraji Zai Rage Radadin Bashin Da Ake Bin Najeriya – Ministar Kudi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ministar kudi, kasafi da kuma tsare-tsare Zainab Shamsuna Ahmed, ta ce hanyar da ta dace na ragewa kasar ɗimbin basuka da ake bin ta shine biyan kudin haraji da kuma shawo kan matsaloli da ake samu na kudaden shiga.

Zainab ta bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, a wurin taron ƙarawa juna sani kan yadda ake kashe kudaden haraji da kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta shirya.

An ruwaito cewa an shirya taron ne kan bijiro da tsare-tsare na yadda za a yi amfani da kudaden haraji da kuma sanya ido kan miƙa bayanai kan kudin tsakaninn mambobin kasashen ECOWAS.

Ministar wacce ta samu wakilcin wata babbar darekta a ma’aikatar, Fatima Hayatu, ta ce gwamnati ta damu matuka kan yadda ake kashe kudaden haraji.

Idan za a iya tunawa dai, a watan Yuli ne, gwamnati ta sanar da cewa bashin da ake bin kasar ya zuwa zangon farko na wannan shekarar ya kai naira tiriliyan 1.94 wanda kuma ya zarta yawan kudaden shiga da aka samu na naira biliyan 310 a lokacin, inda hakan ya nuna cewa basukan da ake bin Najeriyar ya zarta kudaden shiga da take samu a yanzu.

Labarai Makamanta