Birtaniya Ta Sanya Ranar Bada Sanda Ga Sarki Charles III

Za a yi shagalin bikin nadin sarautar Sarki Charles III a ranar Asabar 6 ga watan Mayun 2023. Za a yi shagalin ne a Westminster Abbey, kamar yadda fadar Buckingham ta sanar.

Takardar da iyalan gidan sarautar suka fitar mai taken, “Nadin sarautar Mai Martaba Sarki.” Takardar tace: “Fadar Buckingham na farin cikin sanar da cewa za a yi nadin sarautar Mai Martaba Sarki a ranar 6 ga watan Mayun 2023. “Za a yi nadin sarautar a Westminster Abbey dake Landan kuma Archbishop na Canterbury ne zai jagoranci nadin’.

“A shagalin za a ga yadda za a nada Mai Martaba Sarki Charles III tare da Sarauniyarsa. “Nadin sarautar zai duba rawar da basaraken ya taka a yau kuma zai duba na gaba yayin da ake kafa tsohon tarihi.

Labarai Makamanta