Birnin Gwari Ya Dace Ka Tare Ba Kano Ba – Ganduje Ga El Rufa’i

A jiya ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa ranar Sallah da kansa zai je ya tare hanyar Kano dan kar kowa ya shigar masa jiha daga Kanon.

Gwamnan ya bayyana hakane a yayin jawabin da yayiwa mutanen jihar tasa, kamar yadda Wakilin Jaridar Muryar ‘Yanci ya saurara.

Saidai ga dukkan alama wannan magana ba tawa bangaren gwamnatin jihar Kano dadi ba inda daya daga cikin hadiman gwamna Ganduje wani ya mayar wa da gwana El-Rufai martani.

Hadimin gwamnan Kano kan kafafen sada zumunta, Abubakar Aminu Ibrahim ya mayarwa da gwamna El-Rufai martani ta shafinsa na Twitter kamar haka:

“”Ai El rufai Hanyar Birnin Gwari ya kamata kaje ka tsaya ba hanyar kano ba. Anata sace mutane hanyar Birnin Gwari kullum ka kasa komai ashe kana iya zuwa patrol sai hanyar Kano da ka raina. Banda Bata Lokaci waye zaije Kaduna ranar sallah, Wlh abinma abin ban haushi””. Inji shi.

Related posts