Binuwai: Gwamna Da Dattawan Jiha Sun Yi Wa Atiku Tawaye

Labarin dake shigo mana daga Makurdi babban birnin Jihar Binuwai na bayyana cewar Gwamnan jihar Samuel Ortom a ranar Talata ya bayyana janyewarsa daga goyon bayan dan takarar shugaban kasan jam’iyyarsu ta PDP, Atiku Abubakar.

Ortom ya zargi Atiku da rashin martaba shi a matsayinsa na gwamna kuma yana tafiya nesa da manufofin jihar Benue da al’ummar jihar, musamman Dattawan Jihar masu daraja.

Alamu na nuna cewa, Ortom ya kullaci Atiku ne tun bayan martanisa ga wasu kashe-kashe da suka faru a jihar Benue da ake zargin Fulani makiyaya ne suka yi.

Labarai Makamanta