Bin Tafarkin Sardauna Ne Mafita Ga Shugabanni – Tinubu

An bayyana tsarin salon shugabanci na marigayi Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto a matsayin tsari na adalci wanda ya dace shugabannin a wannan lokaci su bi muddin suna neman samun nasara a mulki.

Jigo a jam’iyyar APC ta kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Ahmed Tinubu ya bayyana hakan, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gidan tarihi na Arewa a taron tunawa da marigayi Sardauna da ya gudana a garin Kaduna.

Tinubu ya kara da cewar a zamanin mulkin Sardauna da sauran takwarorin shi na Jihohin Yamma da Gabas wato Awolowo da Ezikwe, sun ɗora ƙasar akan wani tsari na gaskiya da amana, kuma kaucewa daga wannan tsarin shine silar matsalolin da Najeriya ta tsinci kanta yanzu a ciki.

Dangane da ƙalubalen da tattalin arzikin kasar ke ciki a halin yanzu kuwa, Asiwaju Bola Tinubu ya ce har yanzu tattalin arzikin kasar yana da rauni duk da cewa kasar ta fice daga durkushewar tattalin arziki.

Hukumar kididdiga ta kasar a watan Fabarairun da ya gabata ta sanar cewa arzikin da kasar ta ke samar wa cikin gida ya karu da kashi 0.11 a karshen wata hudu na shekarar 2020.

A cewar hukumar ta NBS, ci gaban ya nuna cewa tattalin arzikin kasar ya farfado daga koma bayan da ya samu.

Sai dai a jawabin da ya yi lokacin da ya gabatar da wata takarda mai taken “Rage yawan kudin da ake kashewa kan shugabanci don ci gaban kasa da matasa a arewacin Najeriya bayan annobar korona”, Tinubu ya ce har yanzu da sauran rina a kaba.

Tsohon gwamnan jihar Legos ya ce duk da matakan da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauka, kawo yanzu tattalin arziki kasar yana da rauni saboda akwai mutane da dama da ba su da ayyukan yi.

“Ya yinda kasar ta ke fuskantar kalubale sai aka samu bullar annobar korona wadda ta shafi tattalin arzikin duniya baki daya ciki har da Najeriya” in ji shi.

Sai dai ya jadadda bukatar ganin cewa an zaftare yawan kudaden da ake kashe wa jami’an gwamnati domin ‘yan Najeriya su amfana daga tattalin arzikin kasarsu”.

Da yake Magana game da karuwar tashin hankali a Najeriya, Tinubu ya ce kasar ba za ta iya shawo kan matsalar ma su aikata miyagun laifuka ba, da kuma matasa ma su tada husuma idan ba ta samar mu su da guraben ayyukan yi ba.

Labarai Makamanta