Bikin Sallah: An Tura ‘Yan Sanda Sama Da 4,000 Kano

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Rundunar ‘yan sanda a jihar ta tura jami’anta 4,144 don samar da tsaro a fadin jihar yayin bukukuwan Sallah da zai gudana a yau.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Abdullahi Haruna ya fitar a ranar Laraba a Kano kuma aka rarraba ta ga manema labarai a birnin Kano.

Haruna ya ce za a tura ‘yan sanda zuwa wurare masu mahimmanci da suka hada da filayen Sallar Idi a lokacin bikin, da sauran wuraren taruwar jama’a.

Kakakin ya ce rundunar tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro da na sa kai cikin farar hula don tabbatar da kariya ga rayuka da dukiyoyin jama’ar Jihar ta Kano.

“Rundunar tana shawartar mazauna jihar da su yi taka tsan-tsan tare da kiyaye shawarwarin tsaro. “Ana shawartar masu bauta da za su je filin Sallar Idi da su guji daukar wasu abubuwa marasa amfani wadanda za su iya haifar da zargi ko fargaba.

“Yara masu kananan shekaru da kuma wadanda ba su da lasisi ba su da izinin yin amfani da motoci, babura masu kafa uku, sauran babura da kekuna yayin zuwa filin sallar Idi.

“Iyaye su kasance tare da yaransu ko su hada yaran da manya yayin da za su je filin Sallar domin duba lamarin yaran da suka bata, hadari ko duk wata mu’amala da ba a so,” in ji shi.

Kakakin rundunar ya yi kira ga kungiyoyi da daidaikun mutane da su guji aikata duk wani abin da zai kawo cikas ga zaman lafiya, yana mai gargadin cewa za a kama wadanda suka saba doka kuma a hukunta su.

Ya kuma bukaci mazauna yankin da su kiyaye ka’idojin Korona, gami da sanya takunkumin fuska da kiyaye tazara tsakanin jama’a a duk lokacin bikin. A cewarsa, rundunar ta fara gudanar da sintiri mai tsauri tare da kai samame maboyar masu aikata laifuka don kauce wa keta zaman lafiya daga masu aikata laifi da bata gari a jihar.

Labarai Makamanta