Bikin Maulidi: Buhari Ya Bukaci Al’umma Su Sanya Kasa Cikin Addu’a

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’ummar Musulmi da sauran jama’ar ƙasa baki daya da suyi amfani da ranar bikin Maulidi wajen sanya Najeriya cikin addu’a na Allah ya fitar da kasar daga matsalolin da ta ke ciki.

Buhari ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da yayi kan bikin ranar Maulidi, wanda mai bashi shawara kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar.

Shugaban ya bukaci al’ummar musulmi da su dage wajen yin koyi da halayyar Manzon Allah SAW na yafiya da tausayi ga jama’a domin cimma nasarar da ake nema.

Hakazalika shugaban ya yi amfani da wannan lokaci inda ya jinjinawa kwazo da kokarin da jami’an tsaron kasa ke yi na yakar matsalolin tsaro.

Buhari ya bada tabbacin yin dukkanin mai yiwuwa wajen shawo kan matsalolin dake addabar Najeriya, inda ya yi kiran samun goyon baya a dukkanin bangarori na ƙasa domin kai wa ga gaci.

Daga karshe Shugaban ya yi roko ga masu amfani da hanyoyi su kula a yayin gudanar da tuki domin kaucewa shiga hatsari da ka iya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Labarai Makamanta