Bidiyon Dala: Ganduje Ya Sake Maka Jaafar Jaafar Gaban Kuliya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Gwamnan jihar Kano, Abdulllahi Umar Ganduje ya sake yin karar Jaafar Jaafar da jaridar Daily Nigerian a wata babban kotun Abuja bisa zargin bata masa suna kan Bidiyon karbar Dala.

A watan Oktoban 2018, jaridar Daily Nigerian da ke wallafa labaranta a shafin intanet ta wallafa wasu fayafayen bidiyo da ke nuna gwamnan yana saka dalloli a aljihunsa da ake zargin cin hanci ne da dan kwangila ya bashi.

Bayan hakan, gwamnan ya yi karar mawallafin jaridar yana mai neman kotu ta tabbatar da cewa abinda Jaafar Jaafar da Daily Nigerian suka yi na ‘wallafa maganganu da bidiyon karya a kafafen watsa labarai da cin mutunci da bata suna wanda ya shigar da karar laifi ne.’

Idan za a iya tunawa, babbar kotu a jihar Kano, a ranar 6 ga watan Yuli ta umurci gwamnan Kano ya biya Daily Nigerian da mawallafinta N800,000 bayan ta yanke shawarar janye karar daga kotu.

A halin yanzu, akwai wata karar a kotu da aka shigar game da gwamnan na Kano inda dan jaridar ke neman a biya shi Naira miliyan 300 domin bata masa suna.

A takardar kara mai dauke da kwanan wata na 15 ga watan Yuli da wakilin Daily Nigerian ya gani, kotun ta bukaci jaridar da mawallafinta su gabatar da takardar bawa lauya izinin ya wakilce su a kotu.

Takardar ta ce: “Ana umurtar ka cikin kwanaki 14 bayan wannan takardar ka umurci a shigar da izinin a wakilce ka a karar da aka shigar kan Dr Abdullahi Umar Ganduje ta yadda za a iya yanke hukunci koda baka nan.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply