Bazoum Ya Lashe Zaɓen Shugaban Kasar Nijar

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa Bazoum Mohamed na jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki ne ya lashe zagaye na biyu na zaben da aka gudanar ranar Lahadi.

Alkaluman da hukumar zabe mai zaman kanta ta CENI ta fitar dazun nan sun nuna cewa Bazoum ya samu sama da kuri’a miliyan 2 da dubu 501.

Dan takarar jam’iyyar RDR Tchanji Mahamane Ousmane, wanda yake biye masa, ya samu kuri’a sama da miliyan 1 da dubu 968.

Wakiliyar BBC da ke Niamey Tchima Illa Issoufou ta ce hukumar zaben ta CENI ta sanar da sakamakon dukkan gundumomi 266.

Bazoum dai ya samu goyon bayan ƴan takarar da suka zo na uku da na hudu a zagayen farko na zaben, shi kuma Ousmane ya samu goyon baya daga gamayyar jam’iyyun hamayya 18.

A ranar Lahadi aka gudanar da zaben zagaye na biyu inda aka fafata tsakanin Mohammed Bazoum da abokin karawarsa Mahamane Ousmane.

Bazoum dai ya samu goyon bayan ƴan takarar da suka zo na uku da na hudu a zagayen farko na zaben, shi kuma Ousmane ya samu goyon baya daga gamayyar jam’iyyun hamayya 18.

A zagayen farko na zaben dan takara Mohamed Bazoum na jam’iyya mai mulki ya samu kashi 39.3 yayin da tsohon shugaba Mahamane Ousmane yake da kashi 16.9 cikin ɗari.

Kungiyoyin da suka sa ido kan yadda zaben ke gudana a kasar sun ce duk da cewa akwai ‘yan kura-kurai da aka tafka, amma an samu ci gaba a bangaren shirye-shiryen yadda zaben ya gudana da kuma yanayin fitowar jama’a wajen kada kuri’a.

‘Yan takarar shugabancin kasa talatin ne suka fafata da juna a zagayen farko na zaben da aka gudanar a karshen watan Disambar 2020 don karbar ragamar mulki daga hannun Shugaba Mahamadou Issoufou, bayan karewar wa’adin mulkinsa na biyu na tsawon shekara goma.

Zaben shi ne irinsa na farko da wani zababben shugaban kasa zai mika mulki cikin ruwan sanyi ga wani takwaransa da za a zaba.

Jamhuriyar Nijar, mai yawan al’uma kimanin muliyan 23, tana daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya a cewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya.

To amma a ‘yan shekarun nan ta gano dimbin arzikin man fetur lamarin da ya kara sanya fata a zukatan talakawan kasar cewa za a yi amfani da arzikin yadda yakamata domin kyautata yanayin rayuwarsu.

Wannan baya ga dimbin arzikin makamashin Yuraniyom da albarkatun noma da kasar ke da su.

‘Yan kasar da dama musamman matasa na fatan samun saukin matsalar rashin aikin yi.

Haka nan zababben shugaban kasar zai tarar da manyan kalubale ta fuskar tsaro – ciki har da tayar da kayar baya na Boko Haram a kudancin kasar kusa da iyakarta da Najeriya, da kuma hare-haren kungiyoyin tayar da kayar baya masu alaka da al-Qa’ida da IS yammacin kasar kusa da iyaka da kasashen Burkina Faso da Mali.

Labarai Makamanta