Bazoum Ya Ɗare Karagar Shugabancin Nijar

Zababben shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, ya sha rantsuwar kama aiki bayan ya lashe zaben da Kotun Tsarin Mulkin kasar ta tabbatar da nasararsa.

Shugaban Kotun Kolin mai shari’a Bouba Mahaman ne ya rantsar da Mohamed Bazoum a gaban mambobin Kotun Tsarin Mulki.

Sabon shugaban kasar ya rantse da Al-Kur’ani mai tsarki yana mai shan alwashin gudanar da mulki bisa doka da oda.

Shugabannin kasashe da na gwamnati da dama ne suka halarci bikin wanda aka yi a Yamai, babban birnin kasar bisa tsauraran matakan tsaro.

An rantsar da sabon shugaban ne kwana biyu bayan wani yunkurin juyin mulki da ya ci tura a kasar. Hukumomi sun ce sun dakile yunkurin na ranar Laraba.

Shugaba mai barin gado Issoufou Mahamadou ya mika wa sabon shugaban kasar tutar Jamhuriyar Nijar da ke nuna sauya mulki daga hannusa zuwa hannun Mohamed Bazoum.

Wannan ne karon farko a tarihin dimokradiyyar Jamhuriyar Nijar da gwamnatin farar hula take mika mulki ga wani zababben shugaban farar hula.

A watan da ya gabata ne Kotun Tsarin Mulkin kasar ta Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da Mohamed Bazoum a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar Nijar da aka yi zagaye na biyu.

Mohamed Bazoum na jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya ya ci zaben da kashi 55.66 cikin 100 na kuri’un da aka jefa abin da ke nufin ya zarce tsohon shugaban kasar kuma dan takarar jam’iyyar Tchanji Alhaji Mahamane Ousmane, wanda ya samu kashi 44.34.

Sai dai Mahamane Ousmane ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben.

Labarai Makamanta