Bayan Tunkarar Rabin Shekara,El Rufa’i Ya Bada Umarnin Bude Wuraren Ibadah

Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, ya dage dokar hana Sallah a Masallatan Khamsu-salawati da zaman coci-coci a fadin jihar.

A takardar da mai magana da yawunsa, Muyiwa Adeleye, ya sanyawa hannu, ya ce an yanke dage dokar ne bisa shawarar kwamitin yaki da cutar Korona a jihar.

Jawabin yace wajibi ne a rika bin dokokin da aka gindaya wanda ya hada da “sanya takkunkumin rufe fuska, baiwa juna tazara, tsafta, wanke hannu, nisanta taron jama’a masu yawa, cin abinci mai kara karfin garkuwa jiki, da zama a gida.”

Gwamnatin ta yi gargadin cewa “wuraren ibadan da suka sabawa ka’idoji da sharrudan da aka gindaya na iya fuskantar sake rufewa domin kare rayukan jama’a.”

Gwamnatin jihar ta sanya dokar kulle Masallatai da coci-coci a jihar Kaduna a ranar 26 ga Maris 20220, doin takaita yaduwar cutar Korona. Daga baya aka sassauta dokar inda aka amince Musulmai su halarci Sallar Juma’a kadai kuma Kirista su hallarci Coci ranar Lahadi kadai.

Jama’ar jihar Kaduna dai sun tunkari kimanin rabin shekara wato watanni shidda kenan suna rayuwar zaman kulle ba tare da halartar wuraren ibada na yau da kullum ba.

Bayan samun wannan sanarwa jama’ar jihar sun nuna matukar jin dadi da farin cikin su, kuma tuni aka buɗe masallatai jama’a suka fara haɗa sahu.

Labarai Makamanta