Bayahuden Da Ya Yi Zanen Batanci Ga Annabi Ya Mutu A Kasar Denmark

Mai zanen shaguben nan a jarida dan kasar Denmark Kurt Westergaard, wanda aka fi saninsa saboda zanen da ya yi na Annabi Muhammad (SAW) wanda ya janyo ce-ce-ku-ce, ya mutu.

Ya mutu yana da shekarun 84.

An wallafa zanen ne a shekara ta 2006, kuma fafutikar da Musulmi masu raji suka yi ta kai ga zanga-zanga wadda ta rikide ta zamo tashin hankali a kasashe da dama na Musulmai.

A baya an yi hakon Westergaard don kashe shi, kuma ala tilas ya arasa rayuwarsa a wani mazauni na sirri tare da kariyar ‘yan sanda.

Sake wallafa zanen a mujallar nan ta zambo ta kasar Faransa wato Charlie Hebdo a shekarar 2015 ya sa an kai wa ofishinta hari inda masu kishin Islama suka kashe mutane 12.

Labarai Makamanta