Hukumar rundunar Yan’sandar Jihar Bauchi tasha alwashi kamu wadanda suka kashe dan majalisa mai wakiltan mazaban karamar hukumar Dass, Hon. Musa Mante baraza tare da garkuwa da iyalansa.
Hukumar ta tabbatar da aukuwar wan nan lamari, na kisan gillar da akayi ma dan majalisar a daren jiya Alhamis, a cewar kakakin rundunar yan’sandan DSP Mohammad Wakil, a wani sako da ya tura wa yan’ jarida da safiyar Jumma’an nan ya shaida cewar yan bindigan da ake tsammanin barayi ne sun kuma yi garkuwa da matan mamacin biyu tare da yarsa mai shekara daya da haihuwa.
Ya kuma shaida cewa, sun samo kwanson alburusai guda hudu a lokacin da suka isa inda wan nan al’amarin ya auku, watu a gidan dan majalisar dake karamar hukumar Dass.
Kakakin yan’sanda yace,
“Matansa masu suna Rashida Musa Mante mai shekaru 40 a duniya, da Rahina Musa Mante mai shekaru 35 tare da yarsa mai suna Fausar Musa Mante ‘yar shekara daya.”
Kana Wakil, ya kara da cewa yan bindigan sun Mamaye gidan marigayin ne inda suka kasheshi, ya kuma tabbatar da cewar tunin hukumar yan’sanda ta fantsama bincike don gano wadanda suka aika wan nan ta asa tare da hadin gwiwa da ofishin yan’sanda na yankin Karamar hukumar.
You must log in to post a comment.