Bauchi: ‘Yan Bindiga Sun Harbe Ɗan Majalisa

Wasu ‘yan bindiga dadi da ba a tantance ko su waye ba sun afka gidan Dan Majalisar Dokokin jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Baraza-Dass inda suka masa kisan gilla kana su yi garkuwa da matarsa.

Ana zargin masu garkuwa da mutane ne suka kashe shi a daren ranar Alhamis a gidansa da ke Dass bayan da suka mamaye gidan.

Zuwa safiyar nan ba mu samu jin ta bakin Kakakin Majalisar Dokokin jihar Bauchi ba, sai dai mai magana da yawunsa Abdul Ahmad Bura ya shaida mana cewa rahotonni da ke zuwa musu kenan.

Kawo yanzu matarsa tana hannun ‘yan bindigan.

Cikakken labarin na tafe.

Labarai Makamanta