Bauchi: Uwargidan Gwamna Taja Hankalin Mata Kan Gina Al’umma

Uwar gidan Gwamnan Jihar Bauchi, Hajiya Aisha Bala Mohammed taja hankalin mata da su rika shiga dumu-dumu cikin aikin gina al’umma ta fannoni da suka shafi Jama’a kai tsaye.

Tayi wan nan kira ne a lokacin da take jawabi a wajen taron bikin tunawa da ranar mata ta duniya na shekar 2021 da ya gudana yau a gidan gwamnatin Jihar.

Aisha Bala ta kara da cewa Mata suna da muhimmiyar rawa da zasu taka na ayyukan kula da kiwon lafiya, da bada Ilimi, da kuma Samar da ayyukan yi da zai taimaki rayuwar mata a duk inda suka sami kansu.

Saboda haka tace a irin wannan rana yana da muhimmanci don tunawa da irin gudummuwar da mata ke bayarwa da Kuma irin muhimmanci da suke dashi ta fanin siyasa a kowani mataki.

Itama anata tsokacin kwamishiniyar mata da ci gaban yara kanana na Jihar Bauchin Hajiya Maryam Gidado ta yaba ma matan ta wajen jajir cewa kan abun da ya shafi mata ta wajen ayyukan hannu domin farfado da tattalin arzikinsu dana kasa baki daya.

Gidado ta kara da cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba don haka dole ne mata su tashi tsaye su tsaya da kafafunsu, a rika damawa dasu.

Matan da suka sami halartan taron na bana sun yaba ma Uwargidan Gwamnan kan ayyukanta na alheri ga dumbimanyan Jihar, da kuma yin korafi ga gwamnatin.jihar da ta rika basu fifiko sosai ba maza kadai ba.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta