Bauchi: Uwargidan Gwamna Ta Yi Gargadi Akan Kyamatar Masu Tarin Fuka

Uwar gidan Gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Aisha Bala Mohammed tayi Gargadi ma al’umma da su guji nuna kyaman masu dauke da chutar Tarin fuka

Tayi wan nan gargadin ne a taron tunawa da ranar Tarin fuka na Shekarar 2021 Wanda hukumar kulawa da ciwon sida da Tarin fuka da kuturta ta Jihar, da hukumar tallafin kasar Amurka (USAID) ta shirya aka gudanar a Jihar Bauchi

Aisha tace abunda ma dauke da cutar yake so shine kauna da soyayya wanda hakan zai basu kwarin gwiwa wajen tunkarar yin magani sosai

Uwar gidan Gwamnan ta kara da cewa
matan shugaban kasa Aisha Mohammadu Buhari itace ta basu damar kuwace take ta tabbatar da ganin an yaki wan nan cuta na Tarin fuka, a matsayin su na matan gwamnoni a dukkanin jihohinsu

Har, ila yau Aisha Bala ta nanata cewa ganin muhimmancin Jama’a tare da kare lafiyarsu yasa a kazabesu jagororin yaki da cutar, domin kawar da ita a cikin al’umma baki daya.

Tace hidimar yaki da citar annobarashakon Numfashi ita ta kawo tsaikon Shirin saboda haka dole ne a tashi tsaye wajen wayar ma da mutane kai, ta yadda za’a yaki cutar.

Tun a farkom taron kwamishinan kiwon lafiya Dakta Aliyu mai goro ya jaddada aniyar gwamnatin Jihar kan yaki da citar a fadin Jihar na harsashen Shekarar 2030 karkashin muradin gwamnatin tarayya

Mai goro yace, fiye da mutane 400,000 ne a kasar nan suke dauke da wan nan Tarin fuka, sannan yace akwai dayawa wadanda ba akai ga ganesu ba a sakamakon annobar korona, yace kuma wadansu suna gudun gwajin da akeyi na cutar Kar ace masu suna dauke da ita.

Kana ya ja hankalin mutane tare da basu shawara da zarar sunji alamun kamuwa da cuta, su garzaya imda ake gwaji kyauta ne babu ko kwabon da zasu biya.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta