Uwar Gidan gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Aisha Bala Abdulkadir Mohammed ta bude Sabowar Cibiyar koyarda Sano’oi yau a garin Bauchi, tare da tallafa ma matasa kimanin su sittin ta fannoni dabam-dabam.
Matan gwamnan tace, yin la’akari da bukatar dake akwai na rage radadin talauci a tsakanin al’umma, yasa ta bude wan nan cibiyar a rukunin gidaje na Ibrahim Bako a fadar jihar, tare da fara horar da matasa da mata ta fanin sana’a, irin wanda mutum yake son yi a mazaunin sana’a musamman ma ga marasa galihu.
Hajiya Aisha ta kara da cewa tace wan nan sabowar dama ce matasan suka samu, domin cibiyar zata rika bada shaidar kammala koyon sana a, da kuma basu daman karbar bashin babban bankin Najeriya da ma wadansu kungiyoyi masu tallafa ma al’umma.
“Sabowar cibiyar a garin Bauchi, ina sa ran cibyar koyar da sana’ar zata zama wani sila na habbaka tattalin arzikin matasan da Jihar Bauchi, kai har ma da kasa baki daya” Tayi harsashe.
Bugu da kari uwar gidan gwamnan ta raba hulunan kwano guda dari biyu 200 ga masu hawa babura, don bukatar yau da kullum, ba na kasuwanci ba, domin karin kulawa da kiyaye fadawa cikin mummunan hadari a kan manyan titunan a fadin Jihar
Ana ta jawabin shugaban gidauniyar Al muhibbah Hajiya Ladi Ibrahim tace manufar tallafin shine domin samar da abi yi ga matasa da kuma rage zaman kashe wando.
Tare kara da cewa “yin hakan zaisa su dogara da kansu, kuma zai hana su shaye-shaye, da kuma rage mutuwar zuciya”.
A lokacin taron shugaban hukumar kiyaye haddura (FRSC) na Jihar Bauchi Yusuf Ibrahim yace abun da uwar gidan gwamnan tayi zai taimaka matuka ta wajen kare lafiyar masu amfani da baburan hawa don amfanin yau da kullum a fadin jiha.
Kana da ga karshe ta raba kayyakin tallafin na sana’oi da kudade ga wadansu matasa kimanin naira N25,000 da kayan aikin Kapinta, da kayan yin aski na zamani, dana gyaran takalma, da kayan mesin da dai sauransu duk a wajen taron.
Daga Adamu Shehu Bauchi
You must log in to post a comment.