Bauchi: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Dage Dokar Hana Walwala A Yelwa

Daga Adamu Shehu BAUCHI

Biyo bayan samun rahotanni zaman lafiya a cikin anguwan Yelwa da kewaye, Rundunar Yan’sandan Jihar Bauchi ta dage dokar hana yawo a yankin Yelwa da kewaye baki daya dake cikin karamar hukumar Bauchi da sanyin safiyar Talatan nan 14 ga watan Yuni na shekarar 2022.

Sanarwar ta fito ne daga hannun Kakakin Rundunar yan’sandan ta Jihar Ahmed Wakil dauke da sa hannun shi a madadin kwamishinan Yan’sandan Jihar Umar Mamman Sanda

Sanarwar ta Kara da cewa kwamishinan Yan’sanda yanzu an samu natsuwa da zaman lafiya a yankin Yelwan Tsakanin, Lukshi da kuma Unguwan Kusu duk a yankin Yelwan da kewaye

Indai ba a manta gwamnatin Jihar ta kafa dokan Hana zirga zirga na tsawo awa.ashirin da hudu, bayan samun tarzoma da ta barke wacce ta kawo asarar rayukan mutane uku Kan hatsaniya tsakanin matasa akan wata yarinya budurwa da kuma Kona Gidaje da asarar dukiya Mai dubin yawa

Inda daga baya aka sassauta dokan zuwa large 6 Shida na yamma zuwa karfe -6 Shida na safe, bayan an girke Jami’an tsaro sunanta sintirin ko ta kwana, da jannkunne duk wanda aka kama a wake zai Yana wa aya zakinta

Har-ila yau sanarwar tace kwamishinan Yan’sandan ya ziyarci yankin Yelwan inda ya sake tabbatarwa Babu wani abu da ya rage na tashin hankali a yankin a yanzu. Kana yayi masu alkawarin duk wanda ya sake ta da husuma a yankin zai gamu da fushin hukumar.

Sanda yaja hankalin al’umman yankin Yelwan da su rungumi zaman lafiya da junansu da makwabtansu don samun ci gaba mai dorewa

Kwamishin ya roki mutanen da su rika hakuri da yadda suka samu kansu, Kan yace su rika sa Ido duk wani wanda zai kawo tashin hankali ayi maza a sanar da Jami’an Tsaro kafin abun yayi kamari

Yace kowa ya fita yayi yawon sa son ranshi tare da rungumar zaman lafiya a tsanin juna

Labarai Makamanta