Bauchi: PDP Ce Da Alhakin Fasa Mana Allon ‘Yan Takara – APC

Daga Adamu Shehu Bauchi

Wani jigo a Jam’iyyar adawa ta APC a Jihar Bauchi Ukasha Hamza Rahama yace fasa allon hotonan Yan’takarar da akayi a Jihar Bauchi, babu shakka ƴaƴan Jam’iyyar PDP ne suka aikata hakan a cikin daren litinin da ta wuce, a kokowar cikin garin Bauchi.

Da yake ma manema labarai karin bayanin yadda abun ya faru a sakatariyar masu dauko rahotanni da watsa labarai na Jihar, yace yin hakan wani yunkuri ne na karya demokradiyya a Jihar Bauchi.

Kana yace ko kadan ba zasu lamunta ba don haka yake Kira ga Gwamnan jihar Bala Abdulkadir Mohammed da ya ja kunnen yayan Jam’iyyar su kar su kawo abun da yafi karfinsu domin a cewarsa in suka fusata abun bazai yi dadi ba, domin basu jin tsoron kowa, ko. mai da martani, kana yace Amma saboda zaman lafiya yafi komai su ba zasu dauki doka a hannun su ba.

Bugu da kari yace shi Gwamnan da yake ci a halin yanzu shima ya tsinci kansa a irin yadda suka kasance ‘yan adawa a Jihar Amma su ba’ayi masu barnar allon hotonan Yan takarar ba, saboda haka a ja ma yayan Jam’iyyar PDP a fadin Jihar da su guji neman fitina a daidai lokacin da zabe ke karatuwa a dukkan fadin Najeriya.

Har-ila yau Hamza ya Kara da kiran kwamishinan Yan’sanda na Jihar da su gaggauta kamo wadanda suke da hannu a cikin wan nan ta’asar kafin abun yazo ya fi karfin hukuma, domin su Yan Jam’iyyar APC bamu su San ta da husuma bane, ya jaddada.

Yace manyan manual Allona Yan’takarar APC a manyan shatale tale na Jihar duk an tumbuke su ko an farfasa su, Kuma na dantakar Gwamna Nura Manu Soro su akafi cirewa, acewars Yan Jam’iyyar PDP su sani yana da ikon fitowa takarar Gwamna Kuma ya shiga zabe a kowace Jam’iyyar yake so, yace basu isa su cire masa wan nan hakkin ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply