Daga Adamu Shehu
A ci gaba kamfen na neman sake darewa kan kujerar gwamna a karo na biyu Gwamnan Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed yace a lokacin da yake aikin gwamnati da majalisar dattijai zuwa Minista da Kuma zuwa yanzu da yake kan karagar gwamna ya dauki akalla mutanen fiye da dubu aiki a dukkan fadin Najeriya.
Gwamnan yayi wan nan furucin ne a wajen gangamin kampen na zaben dubu biyu da ashirin da uku 2023 dake tafe a karamar hukumar Gyade na yankin arewacin jihar Bauchi
Bala Mohammed wanda ke ci gaba da zagayawa kananan hukumomin da suke yankin Katagum domin neman su bashi dama a karo na biyu, ya kara da cewa zai cigaba da shimfida ma yan’jihar ayyukan alhairi da ya faro a wa’adinsa na farko.
Kana ya jaddada kudirinsa na kammala wasu manyan hanyoyi da suka hada Gyade da sauran kananan hukumomin dake makwabtaka dasu, don ci gaba da habbaka tattalin arzikin yankin da kuma, ababen more rayuwa da walwala
“Ina rokonku kudito ranar zabe ki zabi jamiyyar PDP daga sama har kasa, kar kubani kinya ki zaba min abikan aiki sanatoci da yan majalisun, domin hannu daya baya daukan jinka da ni kadaine nake aiki Amma yanzu lokaci yayi da Zaki zabe mu dukka yanntakara pad domin chanji Mai amfani”
Hamza Koshe Akuyam shine Shugaban jamiyyar PDP a jihar Bauchi yace yan’jihar Bauchi karsu yarda a yi masu sakiyar da ba ruwa ta wajen zaben tumun dare,
kuma wanda ba dan gari ba, a cewarsa dole ne a kawo ci gaban mutanen in har suka zabi dansu ba bakon haure ba, wadanda basu da asali a jihar Bauchi, sunce anan aka haifesu amma babu wanda yasan gidansu ko danginsu, saboda haka jiki magayi.
Magoya bayan jamiyyar PDP a karamar hukumar Gyade sun fito don nuna goyon bayansu, ga takarar Gwamnan a karo na biyu suci gaba da jan’ragamar mulkin jihar baki daya
Kana ya kara da nuna muhimmancin zaben Atiku a matsayin shugaban kasan Najeriya a zaben na dubu biyu da ashirin da uku, dake kara karatowa.
END….
You must log in to post a comment.