Bauchi: Mutanen Guru Sun Firgita A Tunanin Rashin Adalci Daga Gwamnati

Daga Adamu Shehu Bauchi

Al’ummar Kauyen Guru dake cikin karamar hukumar Bauchi dab da fadar Jihar sun shiga cikin zullumi da fargaba cewa Gwamnati baza tayi masu adalci ba wajen biyansu kudaden filayensu da Sojojin Najeria suke shirin kwacewa a hannun su tun bayan shekaru dari Uku da zamansu a wan nan wuri,

Sunyi wan nan furucin ne a lokacin da suke ganawa da jami’an Gwamnati wanda Gwamnan Jihar Bala Mohammed ya aika da nufin su tattauna da mutanen yankin, akan wan nan batu amma abunya faskara.

Shugaban tawagar kuma wanda shine Shugaban hukumar DSS a Jihar Malam Sani Adamu ya jaddada aniyarsu a mazaunin su na wakilan Gwamnati domin zama da mutanen yankin Guru don asamu maslaha ta yadda za ayi wa kowa adalci wajen tashinsu da Kuma Sabon wurin da za’a basu a mazaunin biyan diyyan filayensu da na gonakinsu da kuma gidajen su.

Kana yace tuni Gwamnan Jihar yaji kokensu tunda Sojojin barikin shadawanka sukayi barazanar karban filayen a cewarsu duka yankin Guru da kewaye mallakan barikin soji ne tun a shekarar alif dari tara da saba’in da hudu 1974.

Ana shi jawabi Kwamishinan filaye da sufiyo na jihar Bauchi Yakubu Barau Ningi, yayi bayanin gamsashi a wajen taron yadda Gwamna ya bada izinin a share masu filin jejen Allah wanda ba nisa sosai daga inda za’a tashe su.

Hakan nan ya ce duk abubuwan more rayuwa Gwamnan ya bada izinin a fitar masu dashi, Kamar su hanyoyi da rijiyoyin burtsatse da makaranta da kasuwa da ma gina masu asibiti duk a cikin alkawarin.

Barau ya kara da cewa kowa za’asamar masa da filin gonan sa Kamar girman nashi da ya fada cikin wan nan lisafi, yace su sani Gwamnati tana da iko da kowani irin fili a duk lokacin da yace tana so to dole babu makawa saidai a bata filin, alabarshi a biya mutanen dake zaune a wan nan wurin kudaden da zasu gini a wani wurin da yayi masu.

Anasu mayar da martanin kuwa matasan yankin da tsoffin garin sunyi fatali da wan nan tsari a cewarsu basu Jin za ayi masu adalci a karshen al’amari, shiyasa suke cewa Gwamnati ta sake tunani kan wan nan batu

A cewarsu Sojojin su yanka ta wani gefen da yin katanga domin maganan da ake ciki sunyi nisa da gina katanga da zata lakume dukkan kauyakun da suke cikin wan nan yankin.

Wani matashin shima ya miki yace nan ne mahaifar iyayensu da kakaninsu don haka basu ga dalilin da zai sa atashe su ba yanzu da rana tsaka.

Daga karshe dai zaman ba’acimma matsaya ba kan yadda za yi masu su gamsu su kuma yarda zasu tashi su koma wani wuri na dabam.

Indai ba amanta ba jama’ar yankin Gurun dake kan hanyar Jos daura da Otal din Zaranda sun fito sunyi zanga-zanga kan wan nan batu tare da tare hanyan titin mota daga Bauchi’s zuwa Jos.

Labarai Makamanta