Bauchi: Mutane 20 Sun Ƙone A Hatsarin Mota

A yammacin lahadi ne motoci biyo sukayi taho mu game, akan titin Maiduguri dake garin Bauchi inda pasinjoji ashirin suka rigamu gidan gaskiya nan take.

Shaidun gani da ido since hatsarin wanda ya aiku daidai yan mangorori akan titin zuwa Maiduguri kusa da gari Tirwun kimanin murabba’i uku da isa babban birnin Jihar (3km) wanda a cewar su nan take motocin suka kama da wuta ko kafin Yan kwana-kwana so iso wajen tuni mutum ashirin 20 suka cika, mutum biyukima aka ciresu da ransu.

Hakan wadanda suka ga yadda hatsarin ya faru sunce tsakanin mota ce Mai cin Mutum Shatakwas 18 (Hummer Bus) mallakan (Borno Express) tare da wata Mota kirar Golf mai kalan penti bulu wacce take dauke da mutane daga garin Misau zuwa Bauchi

Haka nan sunce mutanen sun Kone fiye da yadda za a iya gane su, in banda mata su biyu da aka cire su da sauran numfashinsu.

Kakakin Yansanda na jhar Bauchi Ahmed Mohammed Wakil ya tabbatar da aukuwar wan nan mummunan hatsarin inda gawawakin da suka kone aka ajiyesu a mutuware a Babban Asibitin kuyarwa na tunawa da Sir, Abubakar Tafawa Balewa dake cikin garin Bauchin inda Mutum biyun da suke kwance suna karbar magani.

Ahmed Wakil yace a daidai lokacin da ake kokarin bincike kan abun da ya haddasa hatsarin, biyo bayan Kiran gaggawa da suka samu, a cewarsa har yanzu babu cikkaken bayanin abin da jawo wan nan mummunan taho mu game, gaba-da- gaba.

‘Muryar Yanci’ tayi kokarin jin ta bakin hukumar kiyaye haddura ta Jihar Bauchin, tare da aike sakon kar ta kwana zuwa ga shugaban hukimar amma abun yaci tura, inda daga bisani kakakin hukumar Rilwanu Silaiman yace shima baya garin Bauchi a lokacin da wan nan hatsarin ya faru marece, bashi da cikakken Karin bayani dalilin aukuwar hatsarin.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta

Leave a Reply