Bauchi: Muna Rokon Gwamnati Ta Ajiye Siyasa A Fannin ilimi – Hadakar Matasa

Daga Adamu Shehu Bauchi

Hadakan Kungiyar Matasan Jihar Bauchi sun roki gwamnatin Jihar da ta jingine siyasa a hidimar Ilimi don samar da ci gaba mai dorewa ta fanin karatun zamani, musamman na karatun jami’oi a garin Azare da na kwalejin koyar da ilimi karkashin gwamnatin tarayya dake Jama’are dana fanin karatun kiwon lafiya a garin Misau.

Shugaban Kungiyar Matasan Umaru Lauya, yayi wan nan rokon a lokacin da yake ma manema labarai bayani kan wan nan batu a ranar Laraba a sakatariyar Yan’jarida dake Bauchi

Shugaban ya kara da cewa sun fahimci babu wani hubbasa da gwamnatin Jihar tayi a kasa na bayar da wuraren da ya kamata gwamnatin tarayya zata aza Tubalin Gina waddan nan makarantu da aka baiwa gwamnatin jihar domin ci gaba da farfado da hidimar Ilimi a yankin arewa maso gabas.

Yace don haka suke kira da babban murya da gwamnatin jiha karkashin Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ta gaggauta bayar da filayen da za a gina makarantun na sosai ba wai gini na wucin gadi ba, a matsayin inda za’a rika gudanar da hidimar wadan nan karatuttukan.

Ummar Lauya, ya kara da cewa sun san cewa a cikin kasafin kudi na gwamnatin tarayya babu maganan makarantun da aka ba Jihar Bauchi, a cewarsu hakan baya rasa nasaba da rashin bayar da filayen da gwamnatin tarayya zata fara aikin gina makarantun, San nan yace sauran jihohin da aka basu tare da Jihar Bauchi, kaman su Gombe, Jigawa da Plateau tuni an sasu a cikin kasafin kudin na shekarar 2022.

Daga karshe matasan sunce in har gwamnatin Bauchi bata tashi haikan ba to sai dai suji a salansa, daga baya kuma a fara korafi ana zargin gwamnatin tarayya batayi wani abu ba akan gina makarantun na Jihar Bauchi.

Labarai Makamanta