Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Bauchi: Mun Mayarwa Kashi 20 Na Mahajjata Kuɗaɗen Su – Hukumar Alhazzai

Hukumar jindadin alhazai ta jihar Bauchi ta sanar da kashi ashirin zuwa talatin na maniyyatan bana sun karbi kudadensu na ajiya, da kuma fara shirye shiryen aikin hajjin na shekarar 2021.

Shugaban hukumar Alh. Abubakar Babangida Tafida, ya shaida hakan a wata zanyawa da manema labarai a yau a garin Bauchi.

Abubakar Tafida ya ce hukumar alhazai ta kasa ita ce ta bada izinin fara shirye shiryen, wanda yace ana sa ranar tara ga watan tara aiyyukkan hajjin badi zasu fara kankama.

Shugaban ya kara da cewa “Daga hukumar alhazai ta kasa tace na sanar da yan uwa Musulmi da yan jihar Bauchi wanda suke su suje aikin hajji badi cewa hidimarsa da dawainiyarsa zai fara tara ga watan tara, a lokacin gwamnatin tarayya zata bude potal don bada daman duk abin da ya dache a hukumance”

Kana har ilayau Tafida ya shawarci maniyyatan damn cewa hukumar alhazan zata yi amfani da wanda ya riga biyan kudinsa, shi za a fara sauraru kafin yan baya da basu biya ta hanyar ajiyan ba, da kuma tantnacewa bisa ka’idojin hukumar jindadin alhazai.

Kana ya kara da cewa har yanzu kofarsu a bude take, ga duk maniyyacin da yake sun karbar kudin sa na ajiya, wanda annobar korona tasa wasu kasashen baza suyi aikin hajji ba a fadin duniya, in banda ma zauna kasar Saudiyya ko kuma yan asalin kasar.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Exit mobile version