Bauchi: Mun Janye Amincewa Ga Kwamishinan Ilimi Akan Rashin Da’a – Majalisa

Daga Adamu Shehu Bauchi

Majalisar dokokin Jihar Bauchi ta janye amincewar data yi ma Kwamishinan Ilimi na Jihar Dr. Aliyu Usman Tilde a bisa zargin rashin da’a da yayi ma yan’majalisar dokoki a lokacin zaman kariyar kasafin kudin ma’aikatar Ilimi ta jihar.

Majalisar ta dauki matakin ne, a zaman ta na gaggawa a ranar litinin inda tace suna da hurumin amincewa ko kuma akasin haka, tsarin mulki ya basu wan nan damar biyo bayan kudirin da shugaban kwamitin Ilimi na majalisar Babayo Mohammed dannmajalisar Mai wakiltar Hardawa, ya gabatar Kuma ta samu amincewar sauran mambobin ta nan take.

Dambarwar ta samo asali ne lokacin da makalisar ta gayyace shi da yazo kima ta saka lokacin da ma’aikatar Ilimin zata kare kasafin kudinta na shekarar 2022 a Jihar, Amma bai zo ba sai bayan misalin awa daya suna jiransa karfe 10 suka sa, amma sai sha daya suka ganshi, acewar majalisar bayan yazo kuma sai yake tambayar wai su suwaye ne.

“Muna kokarin yi mashi bayani yana, saka mana baki, Yana cewa mu su waye ne, munce mashi mune kwamitin Ilimi na majalisa amma bai sauraremu ba shine muka fice muka ce in lokacin da ya fahimci ko mu su waye sai ya dawo domin zama da mu, Kuma shi yana majalisar zartawa, mukuma muna na dokoki, ya tambaye mu wai mu su waye ne, a gaskiya ya tambaye mu muna ganin ya raina majalisa ta 9 ne kawai”, Inji mambobin.

Bugu da kari suka ce muna da kwana takwas ne kadai ya rage akan aikin da suke yi na kasafin kudin jihar, Shugaban kwamitin ya gaya ma majalisar, nan take suka kada kuri’ar rashin amincewa da wan Kwamishina na ilimi a matsayinsa na memba na majalisar zartawa na jihar, ba tare da wani bata lokaci ba.

Kana Suka ce kariyar kasafin kudin ma’aikatar cewa babban Shugaban na din-din-din yazo ya gabatar da jawabai na kariyar kasafin kudin, ga kwamitin majalisar, saboda su samu su kammala aikinsu cikin lokaci.

Har’ilabyau dan’majalisa mai wakiltar mazabar Disina Sale Jibrin, ya gargadi majalisar da tayi hankali da daukan matakin cikin nazari don gudun fadawa cikin rudanin da za’a iya amfani dashi a gaban kuliya manta sabo, inma hakan ta taso.

Kakakin Majalisar Abubakar Y Sulaiman ana shi tsokacin ya bam-bance cewar suna da hurumin aikata hakan, su yarda da da mutum ko akasin hakan, a cewarsa saboda suna da karfin yin haka a hukumance

Kana Abubakar Y. Sulaiman yace abunda kwamishinan yayi ma.majalisar abun takaici me, dole ne yasa suka dauki mataki, kana ya roki al’ummar Jihar dasu kwantar da hankalinsu Babu abunda zai sa su fasa aiki kan kasafin kudin jihar na shekarar 2022 tunda sunsa lokaci, kuma zasu kammala shi kamar yadda aka shirya.

Labarai Makamanta