Bauchi: Matasa Sun Yi Wa Gwamna Ihun Bama So

Rahotanni daga yankin ƙaramar Hukumar Azare ta Jihar Bauchi na nuna cewar wasu gungun Matasa sun yi wa Gwamnan Jihar Bala Muhammad ihun bama so lokacin da Gwamnan ke kan hanyar zuwa duba wasu ayyuka a ƙaramar Hukumar.

Gwamnan ya tafi duba wasu ayyuka da gwamnatinsa ta bada a sassan jihar a Cibiyar Lafiya Birane na Azare a ranar Alhamis a yayinda mummunan babin ya faru.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa gungun matasan sun cigaba da yi wa Gwamnan ihu duk da akwai jami’an tsaro a wurin sun rika ihu suna cewa ‘Ba ma yi!’ ma’ana ba su goyon bayan gwamnan.

Duk da cewa Gwamna Bala Mohammed bai kula su ba, jami’an tsaro da ke tawagarsa sun kama matasa biyu. Jami’an tsaron sun bi su da gudu bayan sun kama su suka sharara musu mari sannan suka jefa su cikin motar ‘yan sanda.

Wani jami’in rundunar yan sanda ta RRS a jihar Bauchi, wanda ya nemi a boye sunansa ya shaida cewa abinda matasan suka yi rashin girmama na gaba ne.

“Ka duba fa, ta yaya za ka fadawa gwamna gaba da gaba cewa baka son sa kuma baka goyon bayan gwamnatinsa, cin mutunci ne.”

Amma ba a tabbatar ko an saki matasan ba a lokacin hada wannan rahoton.

Labarai Makamanta