Bauchi: Matasa Sun Yashe Gidan Dogara

A ranar Lahadi, wasu bata-gari sun shiga tare da yashe gidan tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da ke kusa da asibitin koyarwa na jami’ar jihar Filato.

Jaridar Punch ta gano cewa, ‘yan daban sun take dokar kullen da gwamnatin jihar ta saka musu inda suke ta kusatwa gine-gine domin neman kayan tallafin korona.

An kai harin gidan Dogara da karfe 9 na safe, wata majiya da ta kasance ganau ba jiyau ba ta sanar da Jaridar Punch.

‘Yan sanda da sauran jami’an tsaron da ke tabbatar da an bi dokar kullen sun yi harbi domin tarwatsa taron matasan amma hakan bai sa an samu nasara ba.

“Sun balle gidan tsohon kakakin majalisar wakilai inda suka kai wa kowa hari, har da kaninsa. Sun dinga diban komai da suka samu.

“Matasan sun kwashe adaidaita sahu, kayan dakuna, kayan wuta da sauransu,” wani ganau ya sanar da The Punch.

Karin baynai na nan tafi

Labarai Makamanta

Leave a Reply