Bauchi: Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Yi Tir Da Cin Zarafin Ma’aikacin AIT

Kungiyar Yan’Jarida reshen jihar Bauchi tayi Allah wadai da cin mutuncin da Yan’sanda sukayi ma wani ma’ aikacin gidan-talabijin na AIT a jihar, Yusuf Damina wanda aka fi sani da suna (Nagari) a yayin da yake gudanar da aikinsa na dauko rahoto akan zanga-zangar da ya’makarantar kwalejin harkokin noma ta jiha suka Shirya.

Wan nan sako ya fito ne da sa hannun shugaban Kungiyar ta Jihar, kwamared Umar Sa’idu tare da kashaidi ga dukkanin gidajen watsa labarai a fadin Jihar, da su kaurace ma duk wani daukan rahoto na Yan’sandan Jihar, har sai baba ta gani.

Haka nan Sanarwar tace, wan nan ba shine karo na farko da Jami’an Yan’sanda suke gallaza ma Yan’jarida ba a kokuwar jihar, kusan shine karo.na biyar a cikin shekara daya kachal.

Wan al’amari ya auku ne a ranar Alhamis a lokacin da Yan makarantar Suka fito zanga-zanga don nuna rashi jin dadin su a makarantar dama wasu bukatu, ga hukumar makarantar, yayin da Yan’sanda wadanda ake kiransu (Rapid Respond Squad RRS ) a turance,

suka isa cikin makarantar suka jima Yan makarantar ciwo, a dalilin haka shi dan’jaridar (Nagari) Suka pasa mashi kai da duka, tare da kwace mashi, (Naurar daukan hoto, kwamputa, Abun daukan murya, wayar salula, da kuma karamar jaka ta hannu da yake ajiye muhimman abubuwansa (Wallet).

Kana kungiya ta nemi hukumar Yan’sandan Jihar da tayi gaggawan biyan kudin maganin da aka kashe a Asibitin, tare da biyan diyyar kudade masu dauyi ma shi wan nan dan’Jarida (Nagari)

A ban garen Yan’sandan kuwa, kwamishinan Yan’sandan jihar Mr. Sylvester Alabi, ya bada ummarni bincike kan aikata ma dan jarida wan nan cin zarafi, tare da biyan kudin Asibitin, da Kuma bada hakuri, inji kakin hukumar Yan’sandan, Ahmed Wakil.

Labarai Makamanta

Leave a Reply