Bauchi: Jami’an Tsaron Gwamna Sun Tsallake Rijiya Da Baya

Daya daga cikin.motocin Jami’an yan’sanda na (Rapid Response Squard, RRS) a turance, dake tawagar Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed sun Tsallake rijiya da baya a Hatsarin mota da ritsa dasu a lokacin ran gadin da Gwamnan yake yi don duba ayyuka a fadin Jihar.

Jama’ar dake wurin da hatsarin ya auku ka suma cikin tawagar wadanda su shaidun gani da ido nesin tabbatar ma da labaran Muryar Yanci’ adai dai lokacin da hadarin a faru.

Wan nan hatsarin ya auku ne a daidai lokacin da Kura ta turnike ya rufe ma direban motar gabansa, a kokarinsu na shigewa gaba don jagorancin tawagar.

Sakamakon hakan motar ta kwace a hannun direban ta wuntsula, inda motar yan’jarida da wasu Yan baya suka Kai daukin gaggawa, aka kwashesu tare da motar daukan majinyata dake cikin tawagar, zuwa Asibitin Bununu dake karamar hukumar Tafawa Balewa

Mutum daya ne ya samu mummunan rauni inda sauran kuma sun Sami kana nan rauni da jin jiki sosai, a halinda ake ciki kuwa tuni antura su Babban Asibitin koyarwa dake harin Bauchi don ci gaba da karbar magani.

Har-ila yau, hanyar da hatsarin ya auku itace wacce ta taso daga Burga na cikin karamar hukumar Tafawa Balewa da zata hade da Yelwan-duguri a Karamar hukumar Alkaleri mai tsawon kilomita (km 62)

Hanyar wanda ake sa ran kammala ta nan bada dadewa ba, inji dan Kwangilar da aka bawa aikin gina hanyar.

Labarai Makamanta