Bauchi: Gwamnati Za Ta Karbi Tallafin Biliyan 30 Don Kare Muhalli

Daga Adamu Shehu Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi zata karbo tallafin zunzurutun kudi kimanin naira Bliyan Talatin 30 daga Bankin duniya don kare muhalli daga gurbacewa a sanadiyan ambaliyan ruwa da yayi ma Jihar katutu a daminan bana da ta shige a mafi yawancin kananan hukumomin Jihar.

Shugaban hukumar Kare muhalli na Jihar (BASEPA) Dr. Kabir Ibrahim ne ya shaida haka a lokacin aikin kwashe kasa da ya mamaye hanyoyi da gonaki a dalilin ambaliyan ruwan sama a Cheledi, cikin karamar hukumar Kirfi

Ya ce maganan ambaliyan ruwa, ya daidaita wurare da dama a fadin jihar Bauchi, inda abun yafi kamari a garin Cheledi chan cikin karamar hukumar Kirfi, a gabashin Jihar wadda take da iyaka da Jihar Gombe, yace shiyasa gwamnatin ta neme wan nan tallafi daga babban Bankin duniya, don aikin ba karami bane

Dr. Kabir yace, a halin yanzu gwamnatin Jihar tuni ta amince zata saka nata kudin naira Biliyan daya 1 a mazaunin kafin al’kalami, Wanda za’asa aciki kasafin kudin shekarar 2022, kafin a samu wadan chan kudade na bankin duniya, “munsan gwamnatin jiha baza ta iya ba ita kadai, shiyasa muka gayyachi Bankin duniya don su tallafa Mana da kudi, Ina har muka saka namu tu za subayar da kudin, kuma Gwamnati ta bada fifiko a wan nan batu”, ya jaddada.

Shugaban karamar hukumar Kirfi Garba Musa Bara, anashi tsokacin kan wan nan al’amarin yace zasu tabbatar da gudumuwarsu don ganin wan nan aiki na kwashe kasa da yashe magudanar ruwa a Cheledi ya kammala, munyi kokarin samun shugaban hukumar kare muhalli ta Jihar, kuma mun dace ya amsa rokonmu, ya gayyatu mutanen don yin wan nan aiki da yake ci mana tuwo a kwarya, mun shirya tsaf don kaucewa aukuwar irin wan nan Ibtila’i a nan gaba”.

Shima yayinnda yake nashi bayanin Hakimin Cheledi Alhaji Sale Bello, ya yabwa Gwamnan Jihar Bala Mohammed Kan namijin kokarin da yayi a lokacin wan nan ambaliyan ruwa a yankin, cikin garin Cheledi, yace a shiye suke kowani lokaci subi doka, tare da biyayya ga Gwamnati mai ci, don ci gaban al’ummarsu

Bugu da Kari al’ummar Cheledi da daukacin karamar hukumar Kirfi, sunnyaba da aikin kwashe kasan cewa yazo daidai da lokacin shiri aikace aikacen noman rani, cewarsu su nomankawai suka sani a rayuwarmu, kuma dashi suka dogara.

Daga karshe sun nuna garin cikinsu da godiya mangwamnatin Bala kauran Bauchi, tare da masu ruwa da tsaki a yankinsu, cewa hakan zai fitar dasu daga kangin wahala na ambaliyan ruwa a yankin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply